Likitocin Najeriya Sun Yi Taron Kara wa Juna Sani Kan Maganin Cutar Daji

ABUJA, NIGERIA -Kungiyar likitoci da ke fadakarwa kan abubuwan da ke kawo cutar daji da kuma hanyoyi kariya ta Najeriya, ta gudanar da taron karawa juna sani kan sabbin hanyoyin maganin cutur daji. Taken taron na wannan shekarar shine ‘Sabunta yadda ake maganin cutar daji a Najeriya.

A duk shekara likitoci a bangaren maganin cutar daji kan hallara don tattaunawa da fadakarwa kan sabbin hanyoyin maganin cutar daji da kuma binciken da ake yi na kimiya game da cutar.

Kwararriyar likita a bangaren maganin daji ta fannin gashi wadda ake kira Chemotherapy a turance Dr. Hannatu Ayuba Usman ta ce irin wannan taron kan zai taimaka wajen wayar da kan jama’a game da cutar daji da maganin ta, da kuma sanin irin hanyoyin da ya kamata abi don samun waraka daga cutar.

Haka kuma taron ya duba yadda za a ba wa masu fama da cutar daji cikakken kulawa ta yadda za suyi rayuwa mai inganci a cikin al’umma kamar a cewar Dr. Shehu Salihu Umar.

Dr. Mustapha Muhammad ya ja hankalin mutanen ne da nuna muhimmancin zuwa asibiti a lokacin da cutar ta soma, hakan zai taimaka wajen shawo kan cutar da kuma magance ta.

Shima Dr. Abba Aliyu Tijjani ya ce sun koyi sabbin hanyoyin kimiya ta yadda zasu rika duba marasa lafiya.

A nasa bangaren kwararre a fanni harhada magunguna Dr. Richard Mishelian ya ce da taimakon gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu yanzu ana samun magungunan cutar daji da rahusa, suna kuma fata nan gaba a rika samun magungunan kyauta.

An ware watan gobe ne a matsayin watan wayar da kan jama’a game da cutar daji.

More News

CBN Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ake Samun Karancin Takardun Kuɗin Naira

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana dalilin da ya sa ake samun karancin takardun kuɗin naira a faɗin kasa baki ɗaya. Hakan na zuwa ne...

Ƴan Majalisar Dokokin jihar Rivers 27 Sun Koma Jam’iyar APC

Yan majalisar dokokin jihar Rivers 27 ne cikin 32 suka sauya sheka daga jam'iyar PDP mai mulkin jihar ya zuwa jam'iyar adawa ta APC. Ƴan...

A lura sosai game da yadda jabun takardun naira suka yawaita—CBN ya gargadi ƴan Najeriya

Babban bankin Najeriya, CBN, ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da kudaden Naira na bogi da ke yawo ba bisa ka’ida ba. Wannan...

Ƴan bindiga sun buɗe wuta kan motar kulob ɗin Sunshine Stars

Ƴan wasa da kuma jagororin kungiya ne suka jikkata a wani hari da ƴan bindiga suka kai kan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Sunshine...