Likitoci sun tsorata da lamarin Kano

Likitoci

Hakkin mallakar hoto
@NCDCgov

—BBC Hausa

Watakila a samu koma-baya a yakin da ake yi da annobar korana, sakamakon ja da baya da likitoci suka yi a asibitin koyarwa na Mallam Aminu da ke Kano.

Likitocin dai su na kukan rashin kayan kariya, lamarin da suka ce yana jefa su cikin hadarin harbuwa da cutar korona.

Likitocin, wadanda ke rukunin masu neman kwarewa a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano sun samu kan su a wani mawuyacin hali a Kano, musamman yadda dawainiya ta karu ta kula da marasa lafiyar da ke kwarara asibitin.

Kuma lama’rin ya ta`azzara a dan tsakanin nan, da aka samu karuwar mutuwar mutane masu yawan shekaru.

  • Coronavirus: Mece ce ita da kuma asalinta?
  • Coronavirus a Najeriya: Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

Dokta Abubakar Nagoma, shi ne shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewar, reshen asibitin Mallam Aminu Kano, wanda ya ce aikin da suke yi ya karu, ga shi suna fama da karancin kayan kariya.

”Mun shiga hadari, marasa lafiya na karuwa kullum tururuwa suke yi gashi an samu mara lafiya da ya yada wannan cutar a asibitin”

Aiki ya tsaya cak saboda baka san me zaka taba ko ka gani, inji Dokta Abubakar.

Shugaban kungiyar likitocin ya ce hukumomin asibitin sun yi bakin kokarinsu wajen samar da makarin fuska da safar hannu da kuma man kashe kwayar cuta na sanitaiza, amma kayan kare jiki baki daya bai samu ba.

Don haka ala tilas, likitocin sun ja da baya, ba kuma yajin aiki suke yi ba, suna kokari ne su kare tasu lafiyar da ta iyalansu da kuma abokan aiki.

Su ma hukumomin asibitin Mallam Aminu Kanon sun tabbatar da batun kalubalen da ake fuskanta a asibitin.

Farfesa Musa Babashani shi ne shugaban sashen ba da magani da ke shaidawa BBC matsanancin hali da suke ciki.

”A kasa da duniyar ma baki daya ana fama da rashin kayan aiki, amma hukumar asibiti da daidaikun mutane na kawo agaji”

Ya ce ana samun tallafi amma gaskiya ba sa isa, amma sun tattauna da kwamitin da gwamnatin Tarayya ta aiko domin lalubo hanyoyin kawo musu dauki.

Asibitin mallam Aminu Kano dai ya zama rumfa sha shirgi, musamman ma yadda marasa lafiya ke zuwa neman magani daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu kasashe makwabta.

A wannan lokacin da aka rufe asibitoci masu zaman kansu saboda cutar korona durkushewar asibitin ka iya zama babban koma-baya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnatin jihar Kano, duka sun yi alwashin tallafa yin tsayin-daka wajen ceto rayukan al`ummar jihar Kano daga annobar korona.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...