Likitoci Sun Sanar Da Fara Yajin Aiki Na Kwana 5

Biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan bukatun su a yanzu haka kungiyar NARD ta Likitoci Masu Neman Kwarewa ta tsunduma wani yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.

Yajin aikin zai fara ne daga karfe 8 na safiyar ranar Laraba 17 ga watan Mayu ya zuwa karfe 8 na safiyar ranar Litinin 22 ga watan Maris.

An ɗauki matakin ne biyo bayan taron shugabannin kungiyar na musamman da aka gudanar ta intanet a ranar Litinin.

A ranar 29 ga watan Afrilu ne likitocin suka bawa gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu kan su biya bukatun kungiyar ko kuma su tsunduma yajin aiki. Wa’adin ya kare ne a ranar Asabar 13 ga watan Mayu.

More from this stream

Recomended