Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Yi Barazanar Fara Yajin Aiki

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta NARD tayi barazanar tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza biya bukatun kungiyar cikin makonni biyu.

NARD ta bayar da wa’adin ne a Æ™arshen taron shugabanninta na kasa ranar Asabar a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Shugabannin kungiyar na kasa sun ce, gwamnatin tarayya taki yarda ta tattauna da kungiyar ko kuma É—aukar wani kwakkwaran mataki kan kara albashin likitocin.

Har ila yau kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin biyan likitocin ariyas na shekarun 2014,2015 da kuma 2016.

Kungiyar ta kuma yi allawadai da kudirin dokar hana likitoci fita kasar waje har sai sun yi aiki a kasar nan na tsawon shekaru 5.

More News

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Ministan tsaro Badaru ya yaba wa gwamnan Zamfara saboda tallafa wa aikin soji a jihar

Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji a Jihar Zamfara.Ministan...