Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta (NARD) tayi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta gaza biya musu buƙatar su.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a ranar Talata cikin wata sanarwa mai dauke da sahannun, Innocent Orji shugaban ta na kasa da aka aikewa ministan lafiya Osagie Ehanire.
A cikin wasikar kungiyar ta ce ta bawa gwamnatin tarayya wa’adi watanni shida da suka wuce kan wasu batutuwa da ta gano kan batun samar da asusun horon yan kungiyar.