Lalong ya yi murabus daga mukamin minista don komawa majalisar dattawa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da murabus din ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong.

Lalong, wanda tsohon Gwamnan Jihar Filato ne, zai zama Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu bayan nasarar da ya samu bayan hukuncin kotun daukaka kara a ranar 7 ga Nuwamba, 2023.

Murabus din ya biyo bayan zaman majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi a makon jiya, kamar yadda wani mai taimaka wa shugaban kasar ya tabbatar.

Lalong wanda lauya ne kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Filato ya sha kaye a zaben da aka fara yi na majalisar dattawa amma ya samu nasara bayan hukuncin kotun daukaka kara.

More from this stream

Recomended