
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar sojin Indiya 20, sai dai kafafen yada labari sun ruwaito Indiya na ikirarin kashe sojojin China ita ma
Indiya da China, kasashe biyu mafi yawan jama’a a duniya – wadanda kuma suke da a ji mafi girma da kuma makaman nukiliya – sun kwashe makonni suna kai ruwa rana game da tuddan Himalayas.
Amma wannan batu ya yi kamari ranar Talata. Rundunar sojin Indiya ta ce sojojin China sun kashe sojojinta uku, cikinsu har da mai mukamin Kanar a wata hatsaniya da ta barke a tsakaninsu.
Da yammacin Talata, kafofin watsa labaran Indiya sun ruwaito cewa an kashe sojojin kasar 20 yayin da su kuma suka ‘kashe na China 43 lokacin arangamar’.
Har yanzu China ba ta tabbatar da yawan dakarunta da aka kashe ba ko wadanda suka jikkata.
Wannan ne karon farko da aka rasa rayuka cikin shekara fiye da 40 da ake takadama tsakanin kasshen biyu kan yankin da ke kan iyakarsu.
Yaya kasashen biyu suka tsinci kansu a cikin sabon rikicin, kuma menee ya haddasa shi?
Zaman tsama
Yankin da aka yi arangamar ta ranar Talata yana kan tsohuwar iyakarsu – wanda ake kira Line of Actual Control ko LAC – tsakanin kwazazzabon Galwan a lardin Ladakh.
Wannan yanki ne da ke lardin Kashmir wanda ake takaddama a kansa, inda aka jibge sojoji suka ake yawan tayar da jijiyoyin wuya saboda ikirarin da kowacce daga cikin kasashen India, Pakistan da kuma China cewa su sua malake shi.
Kwarin Galwan ya kasance wani yanki da ake tayar da jijiyoyin wuya inda dakarun Indiya da na China suke sintiri a wurin, kuma tun daga watan Afrilu dukkan bagarorin biyu sun jibge tankokin yaki da manyan bindigogi da na’urorin harba roka da kuma sojoji a yankin.
Kazalika sun jibge jirage masu saukar ungulu da jiragen yaki.
A farkon watan Mayu, abubuwa sun kara ta’azzara bayan kafafen yada labarai a Indiya sun ba da rahoton dakarun China sun kafa tantuna sun shiga da karnuna da kuma wasu manyan kayan aiki cikin wani yanki da ake kallo a matsayin mallakar Indiya.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Indiya ta gina wani titi na kilomita mai yawa da zai karasa har cikin sansanin sojin samanta wanda ta sake farfado da shi a 2008.
Wannan sabon rikicin ya biyo bayan zargin da Indiya ta yi wa China kan wannan batu, “yayin shirin kwance damarar rikicin da ya gudana a hayin Galwan, an samu wani rikicin taho mu gama a daren jiya da ya yi sanadiyyar jikkata da asara ga bangarorin biyu,” kamar yadda wata sanarwar da sojin kasar ta fitar.
Wani mataki na martani China ta ce “ka da Indiya ta yi gaban kanta ko kuma ta tsokano rigima,” kuma ministan harkokin wajen China Zhao Lijian ya ce Indiya ce ta tsallaka iyakarsu, “tare da kai farmaki ga China abin da ya yi sanadiyyar karawar da aka yi tsakanin dakarun kasashen biyu a kan iyakar”.
Menene asalin rikicin?
Dalilai da dama ne suka haddasa wannan rikici, rige-rigen dabarun cimma manufofinsu ne ainihin sanadin rikicin.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Wannan tafkin wanda ya kai mita 450 na tsakanin yankin da ake wannan rikici ne akai tsakanin manyan kasashen Asiya biyu
Indiya da China suna iyaka da juna ta kusan fadin kilomita 3,440 kuma kowa na shiga yankin dan uwansa.
Tun shekarun 1950 China ta ki amincewa da layin da aka shata na kan iyaka tun lokacin Turawan mulkin mallakar Burtaniya.
Wannan ya janyo wani mummunan yaki a shekarar 1962, wanda ya janyo wulakantar tare da cin galaba kan sojin Indiya.
Ikirari da kuma hamayya ga ikirarin
Tun daga wannan yakin ne kuma kasashen ke sukar juna da mamaye iyakarsu.
Indiya ta ce China ta mamaye kimanin murabba’i 38,000 na iyakarta – wanda yake a cikin yankin da aka yi wannan karawa ta baya-bayan nan.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
A yayin yakin 1962 dakarun China sun hambarar da na Indiya ba tare da wani kai ruwa rana ba
China na ikirarin daukacin yankin Arunachal Pradesh nata ne, wanda take kira Kudancin Tibet.
Akwai kuma wasu sauran bangarori da kasashen biyu ke da banbancin ra’ayi akai wadanda suke a kan iyakar.
An yi ta zaman tattaunawa a tsakani sama da shekara 30 sai dai ba a cimma nasara ba, amma ana ci gaba da zama irin na doya da manja a yankin.
Gina ababen more rayuwa
Domin samun sauki wajen kai dakaru a wannan rikici duka bangarorin biyu suna gina titin jirgin kasa da titunan motoci.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Kasashen biyu na kara kai dakaru ciki har da motoci masu sulke
Karkashin shugabancin Narendra Modi, Indiya ta fara gina wasu manyan tituna, kuma ana ta gaggawar a kammala nan da wa’adin da aka dauka na Disambar shekarar 2022.
Daya daga cikin titunan zai tike zuwa hayin Galwan, inda dauki ba dadin da aka yi ya faru.
Ita ma China na gina irin wadannan tituna a yankin da ke da muhimmanci ga Beijing, wanda zai hade da lardin Xinajiang da ke yammacin Tibet.
Karfin fada a ji a duniya da kuma na yanki
Tattalin arzikin China ya ninka na Indiya sau biyar. China na ganin kanta a matsayin wadda za ta iya maye gurbin Amurka a karfin fada aji a duniya.
Ita kuma Indiya ta rungumi tsarin kasashe masu karfin fada a ji a duniya ba wai kwaya daya ba kacal, wanda take gani tana da rawar da za ta iya takawa a wannan tsarin.
‘Yan siyasar Indiya da masu sharhi sau da dama suna magana kan China kamar karfinsu ya zo daya, ba tare da amsa cewa China na wani gagarumin kokari kan wannan iyaka ba.
Shiri da Pakistan
Indiya ta matukar damuwa da alakar da ke tsakanin China da Pakistan, tare da zargin taimaka wa Pakistan wajen mallakar makamin nukiliya.
Wani babban shugaba a Indiya dan jami’iyyar BJP mai mulki na maganar a kara mamaye yankin Kashmir inda nan ne birnin gudanarwar Pakistan.
Indiya na fargabar cewa a nan gaba za a rika amfani da Gwadar wajen taimaka wa atisayen da China ke yi a Kogin Arebiya.
Matsalar Tibet
Ita ma China na zargin alakar da ke tsakanin gwamnatin Indiya da shugaban Tibentan, Dalia Lama. Wani shugaban addini da ya tsere zuwa Indiya bayan wata guguwar sauyi a Tibet da ba ta yi nasara ba a 1959.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
China na son Indiya ta bar yankin Tibetan
Indiya ba ta kallon gwamnatin Tibet a matsayin mai neman mafaka, amma shugaban gwamnatin na cikin manyan bakin da suka halarci bikin Firaminista Modi a 2014.
China ba ta dauki siyasar bangarancin Indiya da muhimmanci ba, kuma tana ganin kasar a matsayin wadda za ta iya hada kai da abokan hamayyarta kamar Amurka da Japan da Kuma Australiya.
Tattaunawa
A baya-bayan nan, dakarun da ke aikin kariya na kasashen biyu sun ta kai wa juna hari na tsawon lokaci.
A 2013 da 2017, wannan ya jawo wata fito na fito wadda sai da aka kwashe makonni ana tattaunawar diflomasiyya kafin a shawo kanta.
Bayan fito na fito a 2017, Modi da Xi sun yi wata tattaunawa domin shawo kan matsalar da ke tsakaninsu.
Kasashen sun kara wata tattauawa don neman mafita kan rikicin – inda manyan hafsoshin kasashen suka hadu a ranar 6 ga watan Yuni da kuma ranar Talata, bayan wannan arangama.