Labari Mai Cike Da Ban Tausayi, Daga Lawan M Ahmad Karaye

Photo: Zainab Habibu Aliyu

Labarin Zainab Habibu Aliyu daliba a Maitama Sule University Kano ya sani takaici matuka da bakin ciki. Zainab sun shirya tare da mahaifiyar ta da yanuwanta zuwa Saudiya Umrah, sun yi checking jakunkunan su guda uku, sai wasu munafukai cikin jami’an Airport din suka kara musu jaka daya mai cike da kwayar tramadol.

Bayan sun isa kasar Saudiya har sun shiga hotel aka biyo su aka kama Zainab aka wuce da ita fursuna, saboda a tagg number din ta suka sanya. Kamar yadda kuka sani hukuncin ta kisa ne Ko
shekarun da baza su yi kasa da goma ba. Kawai sai ta kira uwar ta tana kuka tana sanar da ita fursuna aka kai ta.

Daga baya sai aka kama wasu ma’aikata suna shirin sanya irin wannan jaka mai dauke da kwaya a jakar wata tsohuwar mai shekaru kusan 80. Daga nan aka shiga bincike. Sai aka gano wasu jamiai da aka zargi da hannun su a ciki:
1- Bako A. Salisu, (Mai daure jaka)
2- Rhoda Adetunji, (wadda ta gano cewa suna ragowar kilo)
3- Sani Suleiman (Mai tura hotunan jaka ta WhatsApp)
4- Idris Umar ko Umar Sanda, (wanda aka turawa)
5- Alhaji Gabari, (wanda aka zargi shine mai jaka)
Shi dai Alhaji Gabari ba’a kama shi ba har yanzu.

Abun takaicin shine; mutum nawa aka tura fursuna wasu ma aka kashe akan mugun aikin wadannan mutane, ya’ya nawa suka zama marayu, Mata nawa suka zama zawarawa, iyalai nawa suka yi kuka? Wai shin ma kasar Saudiya za su yarda da wannan bincike ko zai ceto mutane da dama da suke daure
a kurkukun su? Shin wa zai biya diyyar wanda aka hallaka ba tare da laifi ba?

Ya Allah ka sakawa wanda aka zalumta cikin ba da hakki ba.

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da Æ´an ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an Æ´an sanda da kuma sojoji suna É—aukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar Æ´an sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe É—an Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa HaÉ—in Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...