‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

0

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana da matukar hadari.

A karshen makon jiya ne gwamnatin ta sanar da wannan mataki tana mai cewa ta dauke shi ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.

Sai dai wani masani kan harkar tsaro a yammacin nahiyar Afirka, Audu Bulama Bukarti, ya ce shawarar da gwamnatin Zamfara ta yanke za ta iya kawo kazancewar rikici tsakanin Hausawa – mazauna cikin garuruwa da Fulanin daji – wadanda ke zargin ana masu rashin adalci.

Ya ce: “Yanzu haka Fulani na koke-koken cewa ‘yan banga na Hausawa sukan je rugage ne su kashe duk Bafulatanin da suka gani, su kona dukiyarsa saboda suna ganin duk Bafulatani yana cikin ‘yan bindiga.”

“Haka kuma Hausawa mazauna cikin gari suna zargin cewa ana kashe su da garkuwa da su ne saboda kabilanci da Fulani suke nuna masu,” a cewarsa.

Ya kara da cewa idan aka ce kowa ya dauki bindiga to kuwa duk Bafulatanin da Hausawa suka gani a daji kashe shi za su yi, haka nan ma duk Bahaushen da Fulani suka gani su ma kashe shi za su yi.

Bayanan hoto,’Yan bindiga sun addabi kauyukan jihar Zamfara

Saboda haka a cewar Bukarti ya kamata gwamnatin tarayyar Najeriya ta ja kunnen gwamnatin Zamfara kan wannan mataki da ta dauka.

Domin ya ce matakin kyale kowa ya dauki bindiga zai bai wa kowa damar yanke hukunci da kuma daukar doka a kan duk wani da ake zargi, koda kuwa ba ya da laifi.

Gwamnatin ta jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya dai, ta ce ne ta bai wa dukkan ‘yan Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

A wata sanarwa da Kwamishinan watsa labaran Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya aike wa manema labarai ranar Asabar, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.

“Hare-haren ta’addanci sun kasance abin damuwa ga jama’a da gwamnatin jiha.

Domin haka ne, don mu magance wannan matsala baki daya a yankunanmu, gwamnati ba ta da zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar shiryawa da kuma mallakar bindigogi domin kare kansu daga ‘yan fashin daji,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta Jihar Zamfara ta ce ita da kanta za ta shige gaba wajen ganin an saukaka wa mutane hanyar mallakar bindiga, musamman ga “manoma domin samun makaman da za su kare kansu.”

“Tuni gwamnati ta kammala shirin raba fom 500 ga masarautu 19 da ke Jihar nan domin bai wa mutanen da ke bukatar mallakar bindigogi domin su kare kansu,” a cewar sanarwar.

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suke fama da matsananciyar matsalar tsaro a Najeriya sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da raba dubbai daga muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here