Kwararru Na Ci Gaba Da Yin Kiran a Saki Wani Mawaki Da Yayi Wakar Batanci

Kwararrun da ke kare hakkokin bil’adama masu zaman kansu a Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga mahukuntan Najeriya da su saki wani matashin mawaki Musulmi da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin ya yi wata wakar batanci.

Hukumar da ke sa ido kan ‘yancin addinan kasa da kasa ta Amurka da ake kira USCIRF a takaice, ta bayyana Yahaya Sharif-Aminu a matsayin mai yin wakokin addini a jihar Kano da ke arewacin Najeriya kuma dan darikar Tijaniyya ne. Wata kotun shari’ar musulunci ta yanke wa mawakin mai shekaru 22 hukuncin kisa a watan Agustan da ya gabata saboda ya yi wata waka ta dandalin WhatsApp inda “ya yabi wani limamin darikar Tijaniya mai suna Ibrahim Niasse har ta kai ga ya daukaka shi gaban Annabi Muhammadu, “a cewar USCIRF.

Kwararrun hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke bada rahotanni da shawarwari kan saba hakkokin bil’adama sun ce wasu gungun mutane sun kona gidansu Sharif-Aminu a ranar 4 ga watan Maris bayan da ‘yan siyasar yankin suka bukaci a kashe shi.

Kwararrun hukumar ta USCIRF sun ce “suna da damuwa matuka game da rashin bin doka da tsari a shari’ar Sharif-Aminu, ciki har da tsare shi ba tare da bashi damar Magana da wani ba ko daukar lauya a yayin shari’arsa ta farko, wadda ba wanda ya san lokacin da aka yi ta.

Daya daga cikin kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya, Karima Bennoune, mai ba da rahoto na musamman a bangaren hakkokin al’adu ta ce, “aiwatar da hukuncin kisa kan bayyana wani abu ta hanyar zane-zane, rubutu ko yin waka ta yanar gozo ya saba wa dokokin kare hakkokin bil’adama na kasa-da-kasa sosai da kuma tsarin mulkin Najeriya.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...