Jagoran jam’iyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai wa tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a ranar Talata a gidansa na Hilltop Mansion dake garin Minna a jihar Neja.
A yayin ziyarar Kwankwaso na tare da wasu yan majalisar ƙasa da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar ta NNPP.
Kawo yanzu babu wata sanarwa da aka fitar dake nuna maƙasudin ziyarar ta Kwankwaso.


