Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan,Alhaji Dahiru Barau Mangal biyo bayan mutuwar mai dakinsa.
A yayin ta’aziyyar jagoran jam’iyar ta NNPP ya bayyana marigayiyar a matsayin mata biyayya.
Kwankwaso na tare da Alhaji Buba Galadima da kuma wasu jiga-jigan jam’iyar NNPP.




