Kwankwaso ya kaddamar da takarararsa a zaben 2019

[ad_1]

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da takarar neman shugabancin Najeriya a babban zaben shekarar 2019.

Dan siyasar ya kaddamar da aniyyar hakan ne a wani filin taro da ke unguwar Jabi a Abuja ranar Laraba.

Sai dai gabanin hakan, a ranar Talata wani jigo a kwamitin yakin neman zaben Sanata Kwanwaso, Kwamred Aminu Abdussalam, ya yi ikirarin cewa hukumomi sun hana tsohon gwamnan jihar Kano din taron siyasa a wurare biyu a Abuja.

Dubban magoya bayan dan siyasar ne suka taru a dandalin da ya bayyana aniyyarsa ta neman tsayawa takarar.

Image caption

Dubban magoya bayan Kwankwaso ne suka halarci gangamin.

Kwankwaso na cikin mutane da dama da ke son PDP ta tatsayar da su takara domin fafatawa da Buhari a 2019.

Ba wannan ne karon farko dan tsohon gwamnan yake neman shugabancin kasar ba.

Ya fara neman takarar ne a zaben 2015, sai dai ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

A cikin watan Yuli ne Sanata Kwankwaso da shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki da wadansu gwamnoni da ‘yan majalisa da dama suka bar APC zuwa PDP.

Image caption

Kwankwaso ya alkawarin kulawa da masa idan ya samu nasara

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...