
Rauf Aregbesola tsohon gwamnan jihar Osun ya yi wata ganawa da tsohon gwamnan jihar Kano kuma madugun jam’iyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a jihar Lagos gabanin zaɓen shekarar 2027.
Wata majiya ta ce ganawar mutanen biyu ta nayar da hankali ne kan tsara dabaru na zaɓen shekarar 2027.
Ganawar ta su na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan da kungiyar siyasar Aregbesola ta Omoluabi Progressive suka sanar da ficewarsu daga jam’iyar APC.
Abosede Oluwaseun mai magana da yawun kungiyar ya ce mambobin kungiyar sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyar ne saboda yadda ake kyararsu, kora da kuma dakatarwa daga jam’iyar.
Ƴan kwanaki bayan ficewar ta su jam’iyar APC ta sanar da korar, Aregbesola daga jam’iyar inda ta zarge shi da yi mata zagon ƙasa.
Aregbesola wanda ya mulki jihar Osun daga shekarar 2010 ya zuwa 2018 a ƙarƙashin jam’iyar APC ya kuma riƙe muƙamin minista a zamanin gwamnatin Buhari.