Kwankwaso Da Tinubu Sun Yi Ganawar Tsawon Sa’o’i 4 A Birnin Paris

Bola Ahmad Tinubu zaÉ“aÉ“É“en shugaban kasa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso É—an takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zaÉ“en shugaban kasa na 2023 sun yi wata ganawa ta tsawon sa’o’i 4 a birnin Paris na kasar Faransa.

A cewar jaridar The Cable da ta rawaito labarin, ta ce ganawar ta mayar da hankali ne kan batun jawo hankalin Kwankwaso ya shiga cikin gwamnatin Tinubu da za a kafa a ranar 29 ga watan Mayu.

Tun bayan lashe zaben Tinubu ya nuna sha’awarsa ta kafa gwamnatin hadin kan kasa ta hanyar bawa Æ´an adawa wasu mukamai a gwamnatinsa.

Ganawar ta kuma mayar da hankali kan zaɓen shugabannin majalisar kasa ta 10 da za a kaddamar a watan Yuni.

Ganawar ta birnin Paris ta fara ne da misalin 12:30 na rana zuwa 04:45 na rana.

Ganawar ta kuma samu halartar Femi Gbajabiamila wanda ake tunanin shi ne zai zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a gwamnatin Tinubu da kuma Abdulumumin Jinin Kofa wanda yake tare da Kwankwaso.

More News

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Ministan tsaro Badaru ya yaba wa gwamnan Zamfara saboda tallafa wa aikin soji a jihar

Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji a Jihar Zamfara.Ministan...