Kwamshinan zaɓen jihar Ogun ya faɗi ya mutu a Abuja

Niyi Ijalaye, kwamishinan  hukumar zaɓe ta INEC a jihar Ogun ya mutu a Abuja.

Kwamishinan zaɓen ya yanke jiki ya faɗi ya mutu a ɗakin otal dinsa a Abuja bayan da aka gudanar da wani taron kwamishinonin zaɓe a hedkwatar hukumar da maraicen  ranar Litinin.

Taron da aka gudanar ƙarakshin jagorancin shugaban hukumar Mahmoud Yakubu ya mayar da hankali ne kan zaɓen gwamnonin jihohin Ondo da Edo da za a gudanar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Rotimi Oyekanmi mai magana da yawun shugaban INEC  ya ce “Abun takaici mun rasa kwamshinan zaɓen jiya bayan taro,”

An ga kwamshinan zaɓen cikin ƙoshin lafiya sanye da kaya ruwan omo  a wurin taron.

Ijalaye wanda ya fito daga jihar Ondo an naɗa shi kwamshinan zaɓe na jihar Ogun a cikin watan Maris na shekarar 2022 bayan da aka sauyawa, Olusegun Agbaje mutumin da ya maye gurbinsa wajen aiki ya zuwa jihar Lagos.

More from this stream

Recomended