Kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 22 ya nutse a jihar Niger

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger ta ce wani jirgin ruwa dake ɗauke da mutane 22 ya kife a karamar hukumar Agwara ta jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito,Salihu Garba shugaban hukumar na cewa jirgin ya dauko fasinjoji daga kauyen Kasabo na karamar hukumar Agwara ya zuwa garin Yauri na jihar Kebbi.

Garba ya ce hatsarin ya faru da misalin karfe 10 zuwa 12 na ranar Litinin.

Ya ce hatsarin ya faru ne ranar da kasuwar Yauri take ci ya kara da cewa ma’aikatan ceto sun gaza ceto ko ɗaya daga cikin fasinjojin.

Ya kuma kara da cewa torokon ruwa mai karfi ne musabbabin hatsarin.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...