Kunkuru mai shekara 80 da mota ta taka a Argungu ya mutu

Kunkuru

Kunkurun nan mai kusan shekara 80 da likitocin dabbobi a Sokoto da ke arewacin Najeriya suka yi wa tiyata bayan mota ta taka a Argungu ya mutu.

Kunkurun ya mutu ne ranar Juma’a da la’asar, a cewar shugaban likitocin dabbobin yankin Argungu, Dr Samiru Ladan Argungu.

Dr Samiru, wanda shi ne ya soma bai wa kunkurun kulawar gaggawa kafin a kai shi Sokoto, ya shaida wa BBC cewa kunkurun ya mutu ne sakamakon rashin kulawa bayan an koma da shi Argungu daga Sokoto inda aka yi masa tiyata.

A cewarsa, kunkurun, wanda mallakin Alhaji Sulaiman Jarma, shugaban ma’aikatan gwamnatin jihae Kebbi ne, ya cika ne saboda “yaron da ya kamata ya kula da shi bayan an yi masa tiyata bai yi hakan ba. Bai gaya mana cewa sun dawo daga Sokoto ba. Akwai alluran da aka rubuta za a rika yi masa amma ba a yi ba.”

Ya yaba wa likitocin da suka yi masa tiyata a Sokoto yana mai cewa da an bi ka’idojin da suka gindaya kunkurun ba zai mutu ba.

Waiwaye

A farkon mako ne mota ta taka kunkurun abin da ya sa bayansa ya karye.

Sai dai likitocin dabbobi a Sokoto sun ceto shi ta hanyar tiyata ranar Laraba.

Shugaban likitocin Dr Nura Abubakar ya shaida wa BBC cewa tiyatar ta yi nasara kuma kunkurun, wanda ya kusa cika shekara 80, yana cikin koshin lafiya kuma za a sake yi masa wani aiki nan gaba.

Likitocin da suka kai shida gami da jami’an jinya sun mayar wa da kunkurun kwanson bayansa.

Ya ce da farko sun bai wa kunkurun taimakon gaggawa ranar Litinin da daddare, sannan aka yi masa tiyata da safiyar Talata.

“Abin da muka yi masa shi ne mun hada wajen da zai iya haduwa da danyen bawon bayan nasa, sannan akwai inda ya tararratse da yawa da ba zai gyaru ba, sai muka samu wani abu muka rufe wajen, in ji Dr. Nura.

Ya kara da cewa tsawon wajen da ya fashe ya kai inci 12, fadinsa kuma ya kai inci bakwai.

Kwanson kunkurun yana ba shi kariya yana kuma yi masa amfani daidai da wajen da kunkurun ke rayuwa.

A cewar Dr. Nura kwanson kunkurun yana taimaka masa wajen sarrafa yanayin zafi da kuma taimaka masa yin iyo a ruwa.

Ya ce yana kuma taimaka masa wajen ba shi kariya daga abin da zai iya fado masa, da kuma manyan dabbobi da suke farautar kanana.

More News

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...

‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana...

2023: Tinubu will prevent APC lawmakers from dumping party, Shettima claims

A former Borno State governor, Kashim Shettima has said the presidential candidate of the All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, has nipped the...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...