Kotun Koli ta saka ranar Alhamis domin yanke hukunci kan daukaka karar da Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP a zaɓen da ya wuce da kuma Peter Obi na jam’iyar LP suka shigar gabanta.
Atiku da Obi na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu da ya bawa, Bola Ahmad Tinubu na jam’iyar APC nasara.
Daraktan yaɗa labarai kotun, Dr Festus Akande shi ne ya tabbatar da haka a ranar Laraba,
A ranar 9 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta kori karar da ƴan takarar biyu suka shigar saboda rashin hujjoji.