Kotun Koli Za Ta Saurari Shari’ar Zaben Gwamnan Kano Ranar Alhamis

Kotun Koli ta saka ranar Alhamis domin sauraren karar shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da aka daukaka kara a gabanta.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf shi ne ya daukaka kara a gaban kotun in da yake kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe da ya ce, Nasiru Yusuf Gawuna dan takarar jam’iyar APC shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Maris.

Daya daga cikin lauyoyin gwamnan, Barista Bashir Tudunwuzirci ya ce an mika musuo takardar sanarwar sauraron karar.

More from this stream

Recomended