Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Jam’iyar SDP Akan Zaɓen Fintiri

Kotun koli tayi watsi da da ɗaukaka karar da Umar Arɗo ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin jam’iyar SDP ya yi inda yake kalubalantar nasarar ɗan takarar jam’iyar PDP, Ahmad Fintiri ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka yi.

A zaman sauraron karar Laraba rukunin alkalai biyar masu sauraron ƙarar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro sun shawarci waɗanda suka ɗaukaka ta hannun lauyansu, Sylvester Imanugbe da su janye ƙarar da suka ɗaukaka.

Rukunin alkalan sun lura ɗaukaka karar bashi da tushe balle makama.

Imanugbe ya janye ƙarar inda kuma kotun tayi watsi da ita.

More from this stream

Recomended