Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu Gwamnoni suka shigar kan canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zuwa ranar Laraba mai zuwa.
Gwamnonin Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara ne dai suka garzaya kotun suna neman a hana Babban Bankin Najeriya CBN daina amfani da tsoffin takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200 daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.
Kotun dai, a yayin zamanta na ranar Laraba ta dage ci gaba sauraron karar har zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairun 2023.
A yayin zaman kotun na yau an samu karin wasu jihohi da suka nemi a saka su a cikin jerin waɗanda suke kara da kuma wasu jihohin dake neman a saka su bangaren waɗanda ake kara.