Kotun Ƙoli Ta Bada Umarnin A Cigaba Da Tsare Nnamdi Kanu

Kotun Koli ta bayar da umarnin da a cigaba da yiwa Nnamdi Kanu shariar da ake masa kan zargin aikata ta’addanci.

Alkalai biyar da suka saurari shariar sun yanke hukuncin ne a ranar Juma’a.

Kanu na tsare ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS tun bayan da aka taso keyarsa daga kasar Kenya a ranar 19 ga watan Yuni na shekarar 2021.

Inda daga bisani gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi a gaban kotu inda take tuhumarsa da aikata ta’addanci.

A ranar 13 ga watan Octoba ne na shekarar 2022 ne kotun ɗaukaka ta kori ƙarar da ake masa inda ta bayar da umarni da a sake shi.

A hukuncin na ranar Juma’a dukkanin alkalan biyar sun amince da soke hukuncin da kotun daukaka karar tayi.

More from this stream

Recomended