Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Sokoto

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da zaɓen, Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Rukunin alkalan kotun su uku sun yi watsi da ɗaukaka ƙarar da jam’iyar PDP da ɗan takararta, Saidu Umar suka yi inda suke ƙalubalantar nasarar da Aliyu ya samu.

Dukkanin alkalan uku sun ce ba su ga dalilan da zai sa su yi gyara ga hukuncin kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan da ya bawa Aliyu nasara ba.

Aliyu da ya yiwa jam’iyar APC takara ya lashe zaɓe da kuri’a 453,661 a yayin da Umar ya samu kuri’a 404, 632.

Amma Umar ya yi zargin cewa gwamnan da mataimakinsa Idris Gobir sun miƙawa hukumar INEC takardun kammala makaranta na jabu domin su samu damar tsayawa takara.

Masu ƙarar sun kuma yi zargin cewa anyi magudi a zaben.

Kotun a hukuncinta na ta tace sun gaza tabbatar da gaskiyar zarge-zarge 6 da suka shigar da kara akansu.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...