Kotun Ƙoli Ta Kori Ƙarar Binani Inda Ta Tabbatar Da Zaɓen Fintiri

Kotun ƙoli ta tabbatar da Ahmadu Fintiri a matsayin halartaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Adamawa.

Rukunin alkalan kotun su biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a John Okoro a ranar Laraba sun kori ƙarar da Aishatu Binani ƴar takarar jam’iyar APC ta shigar gaban kotun.

Kotun ƙolin ta yanke hukuncin cewa ɗaukaka ƙarar da Binani tayi bashi da tushe balle makama.

Kotun ta ce abin da kwamishinan zaɓen jihar ya yi a lokacin zaɓen bai dace ba kuma babban laifi ne.

A cewar kotun bayyana sakamakon zaɓen da kwamishinan ya yi ya nuna a fili rashin ƙwarewarsa saboda jami’in tattara sakamakon zaɓe ne kaɗai doka ta bashi damar fadar sakamu

More from this stream

Recomended