Kotun Ƙoli ba ta bayyana hukuncin da ta yanke kan taƙaddamar zaɓen gwamnan Sokoto ba

A ranar Laraba ne kotun koli ta ɗage hukunci a karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Sa’idu Umar suka shigar kan zaben gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu.

Kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta dage ci gaba da sauraron karar bayan sauraron bahasi daga bangarorin da ke da hannu a cikin karar.

Sai dai kotun daukaka kara da ke Abuja, ta tabbatar da zaben Aliyu.

Umar da PDP sun yi zargin cewa Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir ba su cancanci tsayawa takarar gwamna ba.

Sun kuma yi zargin cewa zaben ba wai kawai an tafka kura-kurai ba ne, ba a ma gudanar da shi bisa ka’idojin da dokar zabe ta 2022 ta tanada ba.

Kotun daukaka kara, duk da haka, ta yi watsi da daukaka karar da suka yi saboda rashin cancanta.

More from this stream

Recomended