Kotu ta yi fatali da ƙarar da aka kai mata na neman tsige Ganduje a matsayin shugaban APC

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Litinin ta yi watsi da karar da ke neman tsige tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani hukunci da ya yanke, ya yi watsi da karar ne a kan cewa mai shigar da karar, kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya karkashin jagorancin wani Saleh Zazzaga, ba ta da hurumin shigar da karar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.

Mai shari’a Ekwo ya ce babu wata sahihiyar shaida da aka gabatar a gaban kotun da ke nuna cewa kungiyar na da rajista da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC), inda ya ce ba a san sunanta ba.

Alkalin ya ci gaba da cewa kungiyar ba ta da hurumin shari’a saboda batun da aka gabatar a gaban kotun ya shafi harkokin cikin gida ne na jam’iyyar APC.

Sai dai lauyan kungiyar, Ayuba Abdul, a wata hira da manema labarai, ya sha alwashin daukaka kara kan hukuncin.

Shi ma da yake magana, Mista Zazzaga ya ce “bai yi mamakin yadda hukuncin ya gudana ba”.

“Duk da haka, za mu daukaka kara kan hukuncin,” in ji shi.

More from this stream

Recomended