Kotu ta umarci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyaki a Najeriya

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta umarci gwamnatin tarayya da ta tsayar da farashin kayayyaki da na man fetur cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ya umarci gwamnati da ta gyara farashin madara, fulawa, gishiri, sukari, kekuna, da kayayyakinsu, ashana, babura da kayayyakinsu, motoci da kayan aikinsu da kuma kayayyakin man fetur, wanda ya hada da dizal, da kananzir.

Alkalin ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake yanke hukunci a wata kara mai lamba FHC/L/CS/869/2023 da mai rajin kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya shigar a kan hukumar kula da farashin kayayyaki da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, wanda aka lissafa a matsayin wadanda ake tuhuma na daya da na biyu.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...