
Kotun sauraren kararrakin zaɓen gwamnan jihar Zamfara ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Dauda Lawal ya samu a zaɓen da aka gudanar..
Lawal ya yi nasara kan abokin takararsa kuma gwamna mai ci, Bello Matawalle a zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.
Matawalle wanda a yanzu shi ne karamin ministan tsaro n ya garzaya gaban kotun inda yake kalubalantar sakamakon zaben.
A hukuncin ta na ranar Litinin kotun ta ayyana cewa karar bata ta da hujja.
Kotun tavkuma bayar da umarnin a biya wanda ake kara kudi har naira 500, 000.