Kotu ta tabbatar da zaɓen Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara dake Abuja tayi watsi da karar Umar Arɗo ɗan takarar gwamnan Adamawa a jam’iyar SDP ya shigar inda yake kalubalantar zaɓen gwamnan jihar Ahmadu Fintiri a ƙarƙashin jam’iyar PDP.

Arɗo da jam’iyar sa sun shigar da kara a gaban kotun sauraren kararrakin zaɓen gwamna bayan da aka ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Mai ƙara ya nemi a soke zaben bisa dogaro da cewa an sabawa dokokin zaɓe, barazana da kuma rikici a lokacin zaɓe.

Amma kuma alkalin kotun Theodora Uloho ta kori karar saboda ba a shigar da ita bisa ka’ida ba.

Arɗo ya daukaka kara kan hukuncin kotun.

A hukuncinta na ranar Talata mai shari’a Ogochukwu Ogaku ya ce kotun ɗaukaka karar ta amince da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.

More from this stream

Recomended