Kotu ta tabbatar da nasarar da Rufa’i Sani Hanga ya samu

Kotun sauraren kararrakin zaben yan majalisar tarayya da na jihohi dake zamanta a Kano ta tabbatar da nasarar zaben da Sanata Rufa’i Sani Hanga ya samu na jam’iyar NNPP a zaben mazabar Kano ta tsakiya.

Dantakarar jam’iyar APC a zaben ranar 25 ga watan Faburairu, Abdulsalam Abdulkarim wanda aka fi sani da AA zaura shi ne ya shigar da kara gaban kotun inda yake kalubalantar ayyana Sanata Rufa’i Sani Hanga na jam’iyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanatan Kano ta tsakiya.

Zaura ta bakin lauyansa, Ishaka Dikko ya roki kotun da ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kuma ta jingine sanarwar da INEC ta yi da ya bawa Hanga nasara.

Da yake yanke hukuncin ranar Litinin jagoran rukunin alkalan da suka jagoranci zaman shari’ar, mai shari’a I.P Chima ya ce mai karar ya gaza tabbatar da zargin da yake yi ciki har da rashin bin ka’idar dokokin zabe saboda haka an kori karar.

Har ila yau kotun ta bada umarnin mai kara ya biya naira 300, 000 ga wadanda ake kara wato INEC, Hanga, NNPP da kuma Ibrahim Shekarau

More from this stream

Recomended