
Hakkin mallakar hoto
Riccardo Savi
Shugaba Peter Mutharika ne aka sake zaba karo na biyu a zaben na Mayun 2019
Babbar kotun tsarin mulki ta Malawi ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben shugaban kasa bayan soke na farko da aka yi a watan Mayun 2019.
Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce an saba dokokin zabe a yayin zaben, don haka dole ne a gudanar da sabon zabe nan da kwana 151.
Sakamakon zaben da aka soke dai ya nuna cewa shugaba mai-ci Peter Mutharika na kan gaba da kuri’u masu rinjayen gaske.
Tun bayan kammala zaben ne ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a kasar har kawo wannan lokaci.
- Za a bai wa fararen hula makamai don yaki da ‘yan ta’adda
- Wani mutum ya tallata kansa a allon talla don samun masoyiya
Jam’iyyun adawa sun kalubalanci zaben, yayin da ita kuma jam’iyyar shugaba mai-ci ta kafe kan cewa lallai zaben ya gudana kamar yadda ake so.
Kasar ta jima tana fuskantar tashin hankalin siyasa tun bayan kammala zaben na bara.
‘Yan takarar dai bakwai ne suka shiga zaben, amma uku ne ake ganin sun fi samun goyon bayan jama’a.
Shugaba Peter Mutharika ya tsaya takarar ne yana neman wa’adi na biyu, amma mataimakinsa Saulos Chilima da kuma Lazarus Chakwera ne suke kalubalantarsa.
A shekarar 1994, kasar da ke kudancin Afirka ta koma tsarin zaben da jam’iyyu da dama ke shiga bayan da aka yi shekara 30 ana mulkin kama-karya.
Duk dan takarar da zai yi nasara yana bukatar fiye da kashi 50% na kuri’un da aka kada.
Mista Mutharika ne ya yi nasara a zaben 2019 da kashi 38.6% cikin 100.
Ga jerin sunayen manyan yan takarar
Hakkin mallakar hoto
AFP
- Lazarus Chakwera – jam’iyyar Malawi Congress Party
- Saulos Chilima – jam’iyyar UTM Party
- Peter Mutharika – jam’iyyar Democratic Progressive Party – shugaban kasar wanda ke neman wa’adi na biyu