Kotu ta soke takarar mai neman gwamnan Kano karkashin PDP

Abba Kabir Yusuf
Image caption

Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta rushe zaben da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar.

Alkalin kotun, Lewis Allagoa ya yanke hukuncin cewa jam’iyyar ta PDP ba ta gudanar da zaben cikin gida ba, saboda haka kotun ta rushe zaben.

Dan takarar gwamnan a jam’iyyar ta PDP, Ali Amin-little, ne dai ya shigar da karar yana kalubalantar yadda aka yi zaben da har Abba Kabir Yusuf ya zama dan takara.

Abba Kabir ne dai dan takarar jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, babban mai hamayya da gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar APC.

Bayan kotun ta soke takarar Abba, yanzu ta ba jam’iyyar PDP daga ranar Litinin zuwa Asabar da ta gudanar da zaben fitar da dan takara.

Wannan na zuwa ne, yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a Najeriya.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...