Kotu ta sauke kakakin majalisar Nasarawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dan jam’iyyar All Progressives Congress a jihar.

Kotun ta kori kakakin ne a ranar Talatar.

Ta kuma bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Sa’ad Abdullahi Ibrahim a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben mazabar Umaisha/Ugya da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

More from this stream

Recomended