Kotu ta sauke gwamnan Filato daga kujerarsa

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta sauke gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, daga kujerarsa.

A hukuncin da ta yanke a ranar Lahadi, babbar mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu, ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta ba dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Nentawe Goshwe takardar shaidar cin zabe.

Mai shari’a Williams-Dawodu ya yi watsi da hukuncin kotun da ta tabbatar da zaben gwamna Mutfwang, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai dace ba.

Har yanzu dai Caleb Mutfwang yana da damar kara kai kara kotun koli idan yana tantamar wannan hukuncin.

More from this stream

Recomended