Kotu ta samu Maman Boko Haram da aikata zamba

QBabbar kotu dake jihar Borno ta daure, Aisha Wakili wacce aka fi sani da “Maman Boko Haram” har tsawon shekaru biyar bayan da aka same ta da aikata zanba cikin aminci.

Ofishin hukumar EFCC dake yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati shiyar Borno, ya sake a gurfanar da Wakili tare da wasu mutane biyu Tahiru Daura da Prince Shoyode a cikin watan Satumba shekarar 2020 inda ake musu tuhuma biyu da suka hada da hada baki tare da karbar kudi ta hanyar zanba.

Mutanen uku sun hada baki inda suka damfari Saleh Ahmed Said na kamfanin Shuad General Enterprises bayan da suka saka ya kawo musu wake buhu 3000 da kundinsa ya kai 71,400,000 a madadin kungiyar agaji ta Complete Care and Aid Foundation.

Bayan ya kawo kayan ne sai suka bi biyansa kudinsa hakan yasa ya garzaya gaban hukumar EFCC domin neman mafita.

Mutanen za su shafe shekaru biyar da biyan tarar miliyan 30 idan kuma basu biya to za su kara shafe shekara 10 a gidan yari.

More News

Sabon gwamnan Taraba ya tsige kantomomin ƙananan hukumomi

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya amince da rusa kwamitin riko na kananan hukumomi goma sha shida na jihar nan take. Rushewar wanda ke kunshe...

Abba Kabir ya kori shugaban hukumar jin dadin alhazan Kano

Kasa da sa’o’i 24 da hawan kujerar shugabancin jihar Kano, da sanyin safiyar Talatar nan ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kori...

Yadda Buhari ya isa Daura bayan zamowa tsohon shugaban Najeriya

A yau Litinin ne shugaba Buhari ya isa mahaifarsa ta Daura bayan mika mulki ga Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Tinubu dai ya zama shugaban...