Mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele a gidan yari na Kuje har sai an kammala tantance bukatarsa ta neman beli.
Emefiele zai ci gaba da zama a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba, lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan bukatar belinsa.
Lauyan sa, Mathew Burkaa SAN, ya gabatar da bukatar neman belin wanda Rotimi Oyedepo ya yi kakkausar suka a madadin gwamnatin tarayya.