Kotu ta hana Ganduje sayar da asibiti

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga sayar da asibitin yara da kuma haihuwa dake unguwar Yan Awaki a cikin babban birnin jihar.

Mai sharia Maryam Sabo ta babbar kotun jiha mai lamba 16 dake Miller Road ce ta bayar da umarnin kan karar da al’ummar unguwar suka kai gaban ta.

Salisu Ibrahim Yan Awaki shi ne ya shigar da karar amadadin wasu mazauna unguwar su 113.

Lauyan mutanen yan Awaki Barista Badamasi Sulaiman Gandu ya roki kotun da ta dakatar da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da Antoni Janar na jihar da kuma karamar hukumar Birni da Kewaye daga shirin su na sayar da asibitin.

Mai shariar ta amince da bukatar mutanen unguwar inda ta bukaci mutanen da ake kara da su dakata har sai ranar da za ta sake sauraron karar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...