Babban Kotun Tarayya dake Abuja ta hana hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati da kuma takwararta ta ICPC kama tsohon gwamnan jihar Zamfara sanata Abdulaziz Yari har sai ta saurari karar da aka shigar gabanta.
Justice Donatus Okorowo wanda ya bayar da umarnin kan bukatar gaggawa da babban lauya, Michael Aondooaa ya shigar gaban kotun a madadin Yari a ranar Litinin.
Har ila yau alkalin ya kuma hana hukumar tsaro ta DSS kamawa tare da tsare Yari.
Mai Shari’a Okorowo ya umarci hukumomin da ake ƙara da su bayyana dalilan su zai hana shi bayar da umarnin a yayin kotun na gaba.
An daga shari’ar ya zuwa ranar 8 ga watan Yuni