Kotu ta bayar da belin Emefiele bayan ya cika sharuɗa

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele bayan da ya cika dukkanin sharudan beli da kotun ta gindaya.

Emefiele wanda ya isa harabar Babbar Kotun Lagos bisa rakiyar jami’an hukumar EFCC  ranar Juma’a ya samu damar tafiya gidansa bayan kammala zaman kotun.

Alƙali Rahman Oshodi wanda ya yanke hukunci kan batun belin ya bayar da belin Emefiele kan kuɗi naira miliyan ₦50 da kuma wasu mutane biyu da za a su tsaya masa kan kuɗi makamancin haka.

Jim ƙadan bayan da aka bayar da belin sai kotun ta shiga sauraron ƙarar da EFCC ta shigar inda lauyoyin masu ƙara suka gabatar da sheda ba farko.

Shedar farko, Monday Osazuwa wanda ma’aikaci ne a CBN ya faɗawa kotun cewa a lokuta da dama tsohon gwamnan babban bankin na CBN ya tura shi ya karbo kuɗi dalar Amurka miliyan 3.

More from this stream

Recomended