Kotu Ta Bada Umarnin Rarara Ya Sake Bayyana A Gaban Ta

Babbar kotun Shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Rijiyar Zaki a Kano karkashin jagorancin, Mai Shari’a,Halhalatul Khuza’i Zakariyya ta bayar da umarnin sake mika sammaci ga fitaccen mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara bayan da ya gaza bayyana a gaban ta.

Ana tuhumar Rarara da kin biyan kuÉ—i har naira miliyan 10 na wayoyin hannu da ya karba ya rabawa mutane daga hannun wani É—an kasuwa, Muhammad Ma’aji.

Lauyan mai kara, Barista I Imam ya faɗawa kotun cewa wanda ake ƙara ya gaza girmama buƙatar kotun na bayyana a a gabanta saboda haka a bada umarnin kama shi.

Amma kuma Imam ya ce ba shi da tabbacin cewa sammacin kotun ya iske wanda ake zargi.

Kotun ta tambayi masinja ta, Isma’il Zuhudu ko ya mika sammacin inda ya tabbatar da cewa ya liÆ™a shi a kofar gidan Rarara kamar yadda kotun ta umarta saboda yinkurin haÉ—uwa da shi a bashi hannu da hannu ya ci tura.

A karkashe alkalin kotun ya sake bada umarnin a mika sammacin ko kuma like shi a kofar gidan Rarara dake unguwar Zoo Road kana ya dage shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Afrilu.

More News

Jihar Neja za ta riÆ™a biyan  ₦80,000 a matsayin mafi Æ™arancin albashi

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya amince a riƙa biyan ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan ya amince da fara biyan...

Jam’iyar NNPP ta lashe zaÉ“en Æ™ananan hukumomin jihar Kano

Jam'iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaÉ“en  dukkanin kujerun Æ™ananan hukumomin jihar Kano 44. Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Jam’iyar NNPP ta lashe zaÉ“en Æ™ananan hukumomin jihar Kano

Jam'iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaÉ“en  dukkanin kujerun Æ™ananan hukumomin jihar Kano 44. Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...