Kotu ta ba wa Emefiele damar yin bulaguro daga Abuja zuwa wasu wurare

Mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya ya baiwa tsohon gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele izinin ficewa daga babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai kotun ta ce dole ne Emefiele ya ci gaba da zama a kasar.

Emefiele, ta bakin lauyansa, Mathew Bukka, SAN, ya bukaci a sauya sharuddan.

Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo, SAN, bai nuna turjiyarsa game da haka ba.

Ya shaida wa kotu cewa ta tabbatar da Emefiele ya rubuta alkawari cewa zai ci gaba da zama a kasar idan aka amince da bukatarsa.

Haka kuma an gyara tuhumar da ake yiwa tsohon gwamnan CBN zuwa 20 daga 6.

A yanzu dai tuhume-tuhumen da aka yi wa Emefiele sun hada da laifin cin amana, damfarar saye da kuma hada baki wajen aikata manyan laifuka.

More from this stream

Recomended