Wata babbar kotun majistare da ke Kano ta bai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili (Singham), umarnin ya damko shahararriyar jarumar fim din Hausan nan mai suna Hadiza Gabon, sakamakon kin amsa kiran da kotun ta yi mata.
A kwanakin baya ne dan uwanta na wasan kwaikwayo, Mustapha Naburaska, ya maka ta a kotu sakamakon zargin barazana da cin zarafi da ya ce jarumar ta masa. Kotun ta nemi Hadiza Gabon da ta gurfana a gabanta amma ta yi kirmisisi ta ki zuwa.
Alkalin kotun majistaren, Muntari Dandago ya kuma umarci CP Singham da ya gabatar da bincike tare duba ko zargin da barazanar da Naburaska ya ke wa jarumar ya kai matakin da za a gabatar da shi a gaban kotu.