Kotu ta ba da belin Abba Kyari

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon kwamandan rundunar ‘yan sandan farin kaya DCP Abba Kyari na tsawon makonni biyu bayan ya shafe watanni 27 yana tsare.

Ana sa ran Kyari zai kammala bikin binne mahaifiyarsa, Yachilla Kyari.

Daga nan ne kotun ta sanya ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu, domin tantance bukatar neman belinsa a shari’ar da ake yi kan tuhume-tuhumen da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta shigar bayan kama shi shekaru biyu da suka gabata a ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Ku tuna cewa mahaifiyar ta rasu ne da sanyin safiyar Lahadi, 5 ga Mayu, 2024, kuma ta rasu ta bar ‘ya’ya 10 (maza biyar da mata biyar), ciki har da Abba, wanda shi ne babban ɗa.

Yayin da Abba Kyari bai samu damar halartar jana’izar mahaifiyarsa ba, mazauna jihar Borno sun fito da dama domin yi wa Yachilla janaza, wanda aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a wannan rana, a shekarar 2022.

Hukumar ‘yan sanda ta dakatar da Kyari da manyan jami’an ‘yan sanda biyu – Sunday Ubua da James Bawa – bisa zargin cinikin hodar iblis.

More News

Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.Ƴan sandan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...