Mai shari’a Haleemah Salman ta babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin a jiya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutane biyar da ke fuskantar shari’a a gaban kotu kan laifin fashin bankin Offa.
Kotun ta kuma yanke wa kowane daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Wadanda aka yankewa hukuncin su ne Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salahudeen Azeez da Niyi Ogundiran.
A ranar 5 ga Afrilu, 2018, sun kai hari kan wasu bankunan kasuwanci da ofisoshin ‘yan sanda a Offa, karamar hukumar Offa, inda suka kashe mutane 32, ciki har da ‘yan sanda tara a cikin lamarin.
Gwamnatin jihar ta gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a gaban kotu bisa laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, fashi da makami da kuma kisan kai.