Kotu ta ƙwace kujerar gwamnan Kano daga hannun Abba Gida-gida

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta kori Gwamna Yusuf, ta bayyana cewa APC ce ta lashe zaben

A wani a wani mataki da ya zo da abin mamaki, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf daga mukaminsa tare da ayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nasir Gawuna a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Wannan hukunci dai ya zo ne bayan da kotun ta cire kuri’u 165,663 da ba su dace ba daga jimillar kuri’un da Gwamna Yusuf ya samu sakamakon rashin hatimi ko sa hannun da ke kan takardun kiri’u.

Hukuncin kotun dai yana da matukar tasiri a fagen siyasar jihar Kano, inda ya haifar da cece-kuce da tattaunawa tsakanin manazarta siyasa da masu ruwa da tsaki.

Hakan ya nuna mahimmancin ingancin zabe da bin doka da oda a demokradiyyar Najeriya.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...