Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas, a ranar Juma’a, ta yanke hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso wa Idris Olarewaju Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, ba tare da zabin ci tara ba.
Mai shari’a Abimbola Awogboro shi ne wanda ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin.
Kafin a yanke hukuncin sai alkali ya tambaye shi game da jinsinsa, sai ya amsa da sauri cewa shi namiji ne.
Alkalin ya yanke hukuncin cewa zaman gidan yarin zai fara ne a ranar 24 ga Maris, 2024, ranar da aka kama shi.