Koriya Ta Arewa ta karyata rade-radin rashin lafiyar Shugaba Kim Jong-un

Shugaban Koriya Ta Arewan ya shiga wani taron jami'iyyar siyasa da ya gudana

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shugaba Kim Jong-un ya san ana yada wannan labaran karyar a aka lafiyarsa

Hukumomi a Koriya Ta Arewa sun ce rahotannin da ake ta yadawa kan cewa shugaban kasar Kim Jong-un na fama da matsananciyar rashin lafiya bayan tiyatar da aka yi masa a zuciya ba gaskiya ba ne.

Kanun labaran da ke cewa Kim na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai ko kuma yana samun sauki daga aikin da aka yi masa, na da wahalar tabbatarwa.

Sai dai Ofishin fadar shugaban kasa a Seoul ya ce babu wata kwakkwarar shaida daga Arewa da ke nuna shugaban mai shekara 36 na fama da rashin lafiya.

Ba wannan ne karon farko da ake yada irin wannan jita-jitar ba kan lafiyar shugaban, wanda kuma kusan ya karade ko ina – sai dai daga baya aka yi watsi da wannan batu.

Yaushe ne aka fara yada wannan jita-jita?

A baya-bayan nan Kim bai halarci bikin cikar kakansa na wajen mahaifi ba da ya gudana a ranar 15 ga watan Afrilu. Wannan daya ne daga cikin manyan bukukuwa da ake yi a kowacce shekara, bikin wanda ya kafa kasar.

Kim Jong-n bai taba kin halarta bikin ba – kuma abu ne mai wahala ya ki halartar bikin kan radin kansa.

Rashin halartar tasa ne ya janyo wannan jita-jita da shaci-fadi da ba za a iya kauce wa ba – wanda ke da wuyar gano dalili.

Tun ranar 12 ga watan Afrilu rabon da Kim Jong-un ya bayyana a kafafen labarai na kasar “a lokacin da yake duba wasu jiragen yaki”. kamar ko yaushe hotunan lokacin sun nuna shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali.”

Mun sani shi ne ya jagoranci wani babban taron siyasa da ya gudana kwana daya gabanin nan, kamar yadda kafar yada labaran kasa ta bayyana. Amma ba a gansa ba.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

An fara yada jita-jitan ne bayan rashin halartar Kim zuwa bikin kara shekarar kakansa na wajen mahaifi

Kafafen yada labarai ba su ambaci zuwansa ba wajen gwajin makamin nukiliyar da aka yi a makon da ya gabata ba. Wanda kusan yake halarta ko da yaushe.

Rahoto kan Koriya Ta Arewa abu ne mai matukar wuya a lokacin da ya kamata, anma an fara samun bullar jita-jitan ne daga rashin halartarsa wannan bikin da ya gabata.

Amma yanzu, yadda ake gudanar da abubuwa a asirce ya fi sama da yadda ake yi bayan an kulle kasar – a karshen watan Janairu saboda cutar korona.

Rahoton farko na rashin lafiyar

Wannan ikirarin da ake yi wa Kim Jong-un an fara ne daga wani rahoton intanet da ya samo asali daga wasu ‘yan kasar da ba sa zaune a kasar ranar Talata.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Daily NK, sun fahimci cewa “shugaban yana fama da matsalar zuciya tun watan Agustan bara, amma abin ya kazanta bayan ziyarar da yakai Mount Paektu”.

Wannan ce madogarar da kafafen yada labarai na duniya suka rike kan tushen jita- jitar.

Kamfanin dillancin labarai sai suka fara yada wannan labari, wannan ce kuma madogarar labaran da suke ta wallafawa, har sai da ma’aikatar sirri da Koriya Ta Kudu da Amurka suka fara bibiyar wannan ikirari.

Sannan wasu kanun labarai masu daukar hankali daga kafafen labarai na Amurka da ke cewa shugaban Koriya Ta Arewa na fama rashin lafiya tun bayan tiyatar ciwon zuciyar da aka yi masa.

kazalika, wani bayanin da gwamnatin Koriya Ta Arewa ta fitar, da wata majiyar China ta sirri – ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa – wannan labaran ba gaskiya ba ne.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Hoton karshe da aka ga Kim a ciki shi ne tun wanda aka dauka a ranar 12 ga wata Afrilu yana duba ayyuka

Ba wani abu ba ne mai muhimmanci a ko wanne irin lokaci wani ya musanta cewa Kim Jong-un an masa tiyatar zuciya.

Bayanai daga Koriya Ta Kudu da China sun musanta zargin cewa shugaban Koriya Ta Kudu na cikin matsananciyar rashin lafiya.

Mafi yawan mutanen Koriya Ta Arewa ba sa sanin bayanin halin lafiyar shugbansu.

Ba wannan ne karon farko ba da yayi batan dabo

A 2014, Kim ya taba shafe har kwana 40 daga farkon watan Satumba ba a ji duriyarsa – wanda ya haifar da wata jita-jita cikin gaggwa, wanda har aka ce an yi masa juyin mulki.

Sannan sai ya kara bayyana a wani hoto da sandarsa.

Kafofin yada labaran kasar a lokacin, sun amsa cewa yana fama da rashin lafiya, sai dai ba su yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana fama da ciwon kafa ba.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wata jaridar Koriya Ta Arewa ta ta wallafa hoton shugaban a watan Oktoban 2014 rike da wata sanda

Menene shirin Kim dame da me gadarsa?

Idon wani abu ya faru ga shugaban Koriya Ta Arewa, babu bayani kwata-kwata game da wanda zai gaje shi.

Dama mahaifin Kim Jong-un ya raine shi ne na tsawon shekaru domin ya shugabanci kasar. Wanda hakan zai iya tseratar da daular Kim.

Ana gani ‘yar uwarsa Kim Yo-jong ce zabin da za ta hau wannan matsayi. Ba kawai don ta fito daga zuri’ar Paektu ba ne wadda ta kafa daular iyalan Kim, a’a don ita ma tana janyo kanun labarai a kafafen yada labarai na kasar.

A watan da ya gabata ne ta gabatar da wani jawabi a cikin mutane a karon farko, amma ana ganinta a ko wanne lokacin manyan taruka a gefen dan uwan nata.

Yanzu dai za mu jira ne mu zuba ido ko Koriya Ta Arewa za ta yi magana kan wannan jita-jitar da ake yada wa game da rashin lafiyar shugabanta.

Amma maganar gaskiya in ana maganar samun bayanai kan shugabanci Koriya Ta Arewa, kawai dai dukkan mu lalube muke cikin duhu.

Image caption

Dama mahaifin Kim Jong-un wato Kim Jong-il ya raine shi ne na tsahon shekaru domin ya shugabanci kasar

More from this stream

Recomended