Kociyan United ba ya son tafiyar Cavani, Alaba zai tafi Madrid, Neymar na tattaunawa

Edin Son Cavani ba ya jin dadi a Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Mahaifin Edinson Cavani ya ce dansa ba ya jin dadin zama a Manchester United

Kociyan Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer ya tashi tsaye domin ganin Edinson Cavani, mai shekara 34, ya ci gaba da zama a Old Trafford a bazara mai zuwa.

Solskjaer na wannan yunkuri ne duk kuwa da rahotannin da ke nuna cewa dan wasan gaban, dan kasar Uruguay na shirin tafiya kungiyar Boca Juniors ta Argentina. Jaridar Mirror ce ta ruwaito labarin.

Manchester United na kuma shirin tattaunawar kulla sabuwar yarjejeniya da dan bayanta Luke shaw, mai shekara 25, wanda ke ganiyarsa yanzu a kungiyar, kamar yadda jaridar ta Mirror ta labarto.

Haka kuma kungiyar ta Old Trafford na harin sayo dan wasan gaba na gefe na Wolves, kuma dan Portugal Pedro Neto, mai shekara 21, in ji jaridar Sun.

Shi kuwa dan bayan Bayern Munich dan kasar Austria, David Alaba na shirin tafiya Real Madrid ne bayan da kungiyar ta Sifaniya ta amince ta rika ba wad an wasan mai shekara 28 albashin fan 165,000 a duk mako da kuma karin garabasa ta fan miliyan 17, kamar yadda Sun ta ruwaito.

Real Madrid ita kuma ta tuntubi Tottenham da Arsenal ne ko suna da sha’awar wasanta na gefe kuma dan Sifaniya Lucas Vazquez mai shekara 29, in ji jaridar Mirror.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
PSG ta sa Neymar ya zama dan wasa mafi tsada a duniya lokacin da ta saye shi daga Barcelona fan miliyan 200 a 2017

Dan wasan Brazil na gaba Neymar, mai shekara 29 na dab da kammala tattaunawar tsawaita zamansa a Paris St-Germain, in da zai ci gaba da zama har zuwa 2026, in ji jaridar Mercato da ta dauko labarin daga Mail.

Barcelona kuwa na son sake bayar da aron dan wasan tsakiya, dan Brazil ne Philippe Coutinho mai shekara 28 a lokacin bazara.

Kungiyar ta ce a shirye take ta saurari tayi daga kungiyoyi, kamar yadda jaridar Mundo Deportivo ta Sifaniyanci ta labarto.

Chelsea na cikin rashin tabbas kan dan wasanta na baya Antonio Rudiger, mai shekara 28, bayan da ya sheda wa kungiyar ba ya da sha’awar tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya, har sai bayan ya san makomar Jamus a gasar Euro 2020, kamar yadda Athletic ta ruwaito daga jaridar Mail.

Tattaunawa tuni ta yi nisa tsakanin Liverpool da tsohon dan bayan Real Madrid da kuma tawagar kasar Argentina, Ezequiel Garay, mai shekara 34, wanda ba shi da wata kungiya tun da ya bar Valencia a kakar da ta wuce, in ji jaridar El Gol Digital da ta ruwaito daga Express.

A kokarinta na rage kudin da take kashewa na albashin ‘yan wasantaNapoli na duba yuwuwar sayar da dan bayanta Kalidou Koulibaly, mai shekara 29 a kan kasa da fan miliyan 69 da ta sa a kan dan Senegal din a baya, wanda ake maganar cewa zai tafi Liverpool ko Manchester United, kamar yadda Gazzetta dello Sport ta ruwaito daga jaridar Express.

Borussia Dortmund kuwa ta ce a shirye take ta sayar dan wasanta na tsakiya, dan Jamus, Julian Brandt, wanda a baya ake rade-radin tafiyarsa Arsenal, a kan fan miliyan 21.5 a kaka mai zuwa, in ji Bild wadda ta labarto daga Team Talk.

Dan wasan tsakiya na Arsenal din Matteo Guendouzi zai koma kungiyar tasa a kaka lokacin da wa’adin zamansa na aro zai kare a Hertha Berlin, ta Jamus saboda kungiyar ta Jamus ba ta da niyyar daukar dan Faransar mai shekara 21 a yarjejeniyar zaman dindindin kamar yadda Bild ta ruwaito daga Mirror.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...