Kocin Munich ya tsawaita yarjejeniyar zamansa a kungiyar

Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mai horas da Bayern Munich, Hansi Flick ya amince ya tsawaita kwantiragin ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar 2023.

Mai shekara 55, ya koma Munich a farkon kakar bana a matsayin mataimakin Nico Kovac.

Ranar 3 ga watan Nuwamba ya karbi aikin horas wa a matakin rikon kwarya, bayan da aka kori Kovac, daga baya ya amince da yarjejeniyar koci zuwa karshen kakar bana.

Filck ya yi nasara a wasa 18 da ya ja ragama daga 21, hakan ne ya sa shugaban kungiyar, Karl-Heinz Rummenigge ya amince da kwazon kocin.

Rummenigge ya ce ”Kungiyar ta yi murna da yadda Hansi Flick ke gudanar da aiki”

”Bayern ta kara habaka karkashin jan ragamarsa, kuma muna taka leda mai kayatarwa, wadda take kawo sakamako.”

More from this stream

Recomended